Tsaro

Mummunar Rana Ga Boko Haram: Dakarun Sojoji Sun Ragargaza ‘Yan Ta’addar Da Kuma Maɓoyarsu A Borno.

Spread the love

Mummunar Rana Ga Boko Haram: Dakarun Sojoji Sun Ragargaza Yan Ta’addar Dakuma Maɓoyarsu A Borno

Hedikwatar tsaro ta kasa ta tabbatar da ragargazar da mayakan Boko Haram suka fuskanta.

Dakarun sojojin sun ragargaza maboyar yan ta’addan a ranar zagayowar ‘yancin kan Najeriya.

Hakan ya faru ne a Maima da Tusuy da ke Warshale da Tongule a Dikwa-Rann ta Borno

Hedikwatar tsaro ta ce dakarun sojojin saman Operation Lafiya Dole ta samu babban nasara ta hanyar halaka tushe da maboyar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas a ranar bikin zagayowar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Manjo Janar Enenche, ya ce a ranar 1 ga watan Oktoba, dakarun sojin sun kashe ‘yan ta’adda masu tarin yawa a maboyarsu a Maima da Tusuy kusa da Warshale da Tongule a yankin Dikwa-Rann da ke Borno.

Ya ce nasarar an sameta ne bayan bayanan sirri da suka samu wanda ya bayyana inda ‘yan ta’addan suke kuma suke samun mafaka.

Kamar yadda yace, dakarun sojin saman sun yi amfani da jiragen yaki masu dauke da bindigogi inda aka ragargaza wuraren buyarsu biyu.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button