Labarai

Mun bayarda Umarnin gudanar da binciken gaggawa kan masu Maulidi da ake zargin sojojin Nageriya sun Kai masu hari bisa kuskure ~Cewar Gwamna Uba sani.

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna ya bayarda Umarnin gudanar da binciken gaggawa kan harin da ake zargin sojojin Nageriya sun Kai masu Maulid Gwamna ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook Yana cewa Na samu labarin tashin hankali da ban tsoro game da wani mummunan lamari da ya faru a kauyen Tudun Biri da ke unguwar Afaka a gundumar Rigasa a karamar hukumar Igabi, inda aka yi kuskuren kashe musulman da suke gudanar da bukukuwan Mauludi tare da jikkata wasu da dama biyo bayan wani harin da jirgin yaki mara matuki na soja ya kai kan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto a yankin. Gwamnatin jihar ta aike da manyan jami’an gwamnati zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki, da kuma tuntubar iyalan wadanda abin ya shafa tare da ba gwamnati shawara kan matakan gaggawa da za a dauka domin rage radadin iyalan wadanda abin ya shafa.

Na ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan wannan mummunan lamari. Mun kuduri aniyar hana sake afkuwar wannan bala’i tare da tabbatar wa al’ummarmu cewa za a ba da fifiko wajen kare su a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka.

Na kuma ba da umarnin kwashe wadanda suka jikkata cikin gaggawa zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko domin samun kulawar gaggawa. Gwamnati za ta dauki nauyin kula da su

Ina kira ga al’ummar da abin ya shafa, da daukacin ‘yan kasa da su kwantar da hankalinsu, mu ci gaba da ba jami’an tsaro da gwamnatin jihar goyon baya, a yakin da muke yi da ‘yan ta’adda, ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun mutane a jihar Kaduna. Ina tuntubar jami’an tsaro domin ganin an kaucewa irin wadannan kura-kurai a ayyukan da za a yi nan gaba.

A Madadin Gwamnati da Jama’ar Jihar Kaduna, Ina Mika Ta’aziyyarmu Ga Iyalan Da Suka Rasa ‘Yan Uwansu. Allah ya jikansa da rahama ya jikan dukkan wadanda abin ya shafa da Aljannar Firdausi, da iyalansu baki daya. Ta’aziyyarmu kuma tana zuwa ga waɗanda suka sami raunuka. Muna musu fatan samun sauki cikin gaggawa Inji Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button