Labarai

Mun ci gaba da mayar da hankali wajen bunkasa rayuwar Al’ummar jihar Zamfara duk da hukuncin kotu – Cewar Gwamna Lawal.

Spread the love

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alkawarin ci gaba da mayar da hankali a yunkurinsa na aiwatar da ayyukan raya kasa a jihar, duk da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na cewa zaben na ranar 18 ga watan Maris bai kammalu ba.

Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi ga kungiyar amintattun jam’iyyar a Gusau jim kadan bayan dawowarsa daga Abuja.

Ba mu da wani abin damuwa; mun san cewa al’umma sun zabe mu a baya, kuma har yanzu a shirye suke su sake zabe mu. Yunkurinmu na ceto jihar Yana nan, domin kuwa za ku ga wasu ayyukan raya kasa da ake ci gaba da yi a fadin jihar Babu Wani Abu Daya Chanja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button