Al'adu

Mun Dasa Bishiyoyi Dubu Uku A Kano A Wannan Shekarar Ta 2020.

Spread the love

Gidauniyar tallafawa mabukata Daga tushe ta gudanar da dashen bishiyoyi Wanda yawansu yakai 3000 a jihar Kano karkashin shugaban Gidauniyar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa.

Shugaban Gidauniyar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa yace dama duk shekara suna gabatar da wannan aiki a dai dai lokacin da damuna zata Kama Daga watan Biyar har zuwa watan 8 na kowacce shekara.

Shugaban Gudauniyar Danlarabawa yace hikimar shine idan sunyi dashe a wannan lokaci suna sa ran idan ruwan damuna ya sauka Akan bishiyoyin da suka dasa da yardar Allah zasu Zama sun Mike kuma zasu rayu ba tare da wata Matsala ba ta rashin ruwa duba ga yadda ake wahalar ruwa a unguwanni daban daban da ake dasu a fadin jihar.

Danlarabawa ya Kara da cewa tsari ne da suke anfani dashi wajen dasa bishiyoyin a unguwanni, Masallatai, da Makarantu dama Asibitoci ko maaikatu da ake dasu.

Auwal Danlarabawa yace wannan dai wata hikima ce da suka kirkira Dan kafa sadaqatul Jariyah Wanda kuma suke hada kudi Dan aiwatar da aikin a junan su, sannan sukan bawa alumma dama Dan shiga tsarin ta hanyar bada gudunmawaba saya musu nasu daban ayi musu wannan dashe na bishiya da sunan su ko iyayen su ko wani nasu da ya Rigamu Gidan gaskiya.

A karshe shugaban Gudauniyar Amb Auwalu Muhd Danlarabawa yayi Kira ga daukacin alumma da su daure su dinga dasa bishiya koda guda Daya ce a kowacce shekara Dan samun lada.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button