Mun gamsu da tsarin mulkin Uba sani na Hikima domin Samar da tsaro tare da kokarin Gina Kauyaku ~Cewar Dattawan kaduna


Dattawan Jihar Kaduna da suka gana da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, sun bayyana cewa Gwamnan ya fara gudanar da mulkin sa bisa kyakykyawan tsari kuma sun ba da tabbacin za su mara masa baya don samun nasara.
Dattawan da suka gana a karkashin kungiyar dattawan jihar Kaduna da manyan ’yan kasa, sun yi alkawarin tallafa wa Uba Sani don samun nasarar kokarinsa na kubutar da jihar daga kangin rashin tsaro, da talauci.
Sun ce sun kuduri aniyar bayar da goyon bayansu ga burin Gwamna Sani na farfado da harkar noma da bunkasa tattalin arzikin karkara.
Da yake magana a madadin dattawan bayan wata ganawa da gwamnan a gidan Sir Kashim Ibrahim Kaduna, tsohon shugaban mulkin soja na jihar River, Janar Zamani Lekwot (Rtd), ya ce gwamna Sani ya fara da kyau, ya kara da cewa a matsayinsu na dattawa aikinsu shi ne bayar da gudummawa. nasiha masu cike da gogewa, suna masu karfafawa bisa gogewar da suka samu a baya.
“Zaman na yau ya kasance mai matukar ban sha’awa cike da gaskiya da bege. Manyan batutuwan sun shafi, rashin tsaro, da yadda za a fitar da jihar Kaduna daga kangin rashin tsaro. Idan aka yi haka, yankunan karkara da birane za su samu ‘yanci ta yadda ‘yan kasa za su rika tafiya cikin walwala don neman jin dadinsu,” in ji Lekwot.