Labarai

Mun Gane Cewa APC Na Jin Dadin Wahalar Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki, PDP Tafadawa APC.

Spread the love

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa jan’iyya me mulki ta APC na jin dadin wahalar da ‘yan Najeriya ke ciki inda take kare tsare-tsaren gwamnatin shugaba Buhari.

A sanarwar da PDP ta fitar ta bakin sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan ta bayyana cewa ta yaya APC zata rika kare karin kudin man fetur da shugaban yayi Naira 80 da zuwa 140? Tace duk wata jam’iyya dsta san abinda take ya kamata ta yi Allah wadai da irin wannan abu.

Tace tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasar sun kashe masana’antun Najeriya da dana inda darajar kudin Naira ya fadi ake sayen dala 1 sama da Naira 400 sannan kuma a karkashin Mulkin shugaba Buhari Najeriya ta zama matattarar Talaucin Duniya.

Yace kamata yayi APC ta baiwa ‘yan Najeriya hakuri kan gaza cika musu alkawuran data dauka amma ba wai kare wahalar da suke ciki ba.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button