Labarai

Mun Gano Makiya Buhari…

Spread the love

Daga marubuci Dattin Assalafy yace ai dama duk soyayyar da aka ginata ba don Allah ba to sai ta ruguje, masoyi na gaskiya bai gudunka don wata jarrabawa ta gitta a tsakani, masoyi na gaskiya zai kasance tare da kai duk runtsi duk wuya, gudun shugaba Buhari da ake ya sa ina kara fahimtar halin mutanen mu mai ban tsoro

Halin da muke ciki; kamar misalin shugaba Buhari direban motar fasinja ne yana tsakiyar gada sai ta karye, maimakon a taimakeshi a fitar dashi don kada ya halaka al’umma su halaka, sai aka juya masa baya ana gudunsa, hatta daga cikin masu ikrarin masoyansa ne, saboda dama soyayyar sun ginata a kan wata manufa na dabam ba don Allah ba

Duk bala’in da muka gani muka shaida a gwamnatin Jonathan bai kai rabin wanda muke gani a gwamnatin Buhari ba, amma duk da haka mutanen Jonathan ba su taba juya masa baya ba, hatta garin Chibok da suka fuskanci mafi munin bala’i ba su juyawa Jonathan baya ba saboda addininsu, Jonathan din suka sake zaba mafi yawansu a zaben 2015, addini ya hadasu da Jonathan suka rike masa amana, sukayi hakuri da jarrabawan da ta afka musu na sace yaransu da akayi

Ina kuwa kai Musulmi? ace mabiyin addinin nasara ya fika hakuri da tawakkali akan jarrabawa? wannan abin kunya ne, bai kamata a samu musulmi da wannan halin ba, ni Datti Assalafiy da makamantana muna son shugaba Buhari saboda Allah ne da kuma addininsa, idan kun samu labarin na dena son shugaba Buhari to wallahi yayi ridda ne, ko kuma zaluncinsa ya bayyana karara a gareni wanda Insha Allahu hakan ba zai taba faruwa ba

Shugaba Buhari tamkar amana yake a garemu saboda Musulunci, juya masa baya kamar cin amana ne, abu mai wahala a wannan zamanin namu shine rikon amana da kuma soyayya na gaskiya saboda Allah, yanzu ma da kuke gudun shugaba Buhari zuwa wani gurin, duk inda kuka je sai kun gujesu, don dama mai hali baya fasa abinsa, duk soyayyar da aka gina ba don Allah ba sai ya rushe

Juyawa shugaba Buhari baya ba mafita bane, abin kunya ne, dabi’ace ta rashin hankuri da rashin dauriya, idan ka san ka bada gudunmawa wajen kafa mutum to taimakonsa zakayi domin ku fita kunya, babu abinda zakayi wanda zaka wanke kanka daga zargi a gurin mutane

Suma ‘yan adawa da ake yin hijira ana dawowa garesu, kuyi hankali, yadda sukayi anan haka zasu muku idan jarrabawa ta sameku, idan bukatarsu bata biya ba zasuci amanarku su dawo manyan makiya a gareku

Yaa Allah Ka shiga tsakanin mu da masoyan karya, Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Ka bashi ikon gyara kuskurensa, Ka raba tsakaninsa da maciya amana, Ka tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button