Labarai

Mun Kama Dreban Dangote Yana Yukurin Saida Trelar Dangote~ Yan Sanda.

Spread the love

Rundunar Yan Sanda a jahar Neja ta cafke mutane hudu 4 da take zargi da yunƙkurin siyar da wata tirela mai lambar rijista KMC 544 XA, dauke da buhuhunan siminti 754, mallakin kamfanin Dangote Portland Cement a ƙkauyen Dikko dake ƙkaramar hukumar Gurara, a jahar ta Neja.

Mai Magana da Yawun Rundunar Yan Sandan Jahar Neja. ASP Wasiu Abiodun ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Juma’a da Tagabata.

Bidiyon ya ce ranar 1 ga Yuli da misalin ƙkarfe 7:45 na dare, jami’an ‘yan sanda dake aiki a Gawun Babangida Division suka cafke wani mutum, Saidu Ayaba mazaunin Ayangba Kogi, wanda direba ne mai aiki da kamfanin Dangote Portland Cement da tirela wadda ba komai a cikinta a Dikko dake ƙKaramar hukumar Gurara ta Jahar Neja. yana ƙkokarin siyar da ita.

A lokacin da muke tambayar sa, wanda ake zargin ya amsa cewa ranar 26 ga Mayu da misalin ƙkarfe 10:00 na safe, an Loda Mashi buhuhunan siminti 900 don ya kai su Depot 3 dake Kano.

Wanda ake zargin sai ya hada baki da wani mutum, Habibu Isah mazaunin Shiyar Numo, dake ƙkaramar hukumar Tsafe ta jahar Zamfara, Mudashiru Dahiru mazaunin ƙkaramar hukumar Madobi dake jahar Kano, da Abdullahi Mohammed, mazaunin ƙkaramar hukumar Biu dake jahar Borno, wanda shi ne bakaniken da ya cire Na’urar da za a iya gano motar a duk inda take, In ji Shi.

Abiodun ya ce Habibu Isah da Mudashiru Dahiru sun taimaka wajen karkatarwa da siyar da simintin ga wani, Aminu mazaunin ƙkaramar hukumar Tsafe dake jahar Zamfara, wanda a yanzu ya gudu da N2,160,000, kuma suka ƙkara hada kai don siyar da tirelar da ba komai a cikin ta.

Mun kama wayanda muke zargin, kuma abubuwan da muka gano sun hada da buhuhunan siminti 754- in ji shi.

Ya ce za a maka waɗanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Daga Ahmad T Bagas.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button