Mun kashe dollar Amurka Bilyan Shida $6bn domin shigo da alkama Nageriya~ Sabo Nanono
Mininstan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono ya ce, gwamnatin Najeriya ta kashe kimanin Dala biliyan shida wurin shigo da alkama daga kasashen waje daga 2016 zuwa watan yuli 2020.
Ministan ya bayyana a wani taro da aka gudanar a Kano, cewa kididdigar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar ne ya tabbatar da hakan. Nanono, ya ce ana samar da alkama kimanin tan 420,000, a cikin gida alhali bukatar da ake da ita ta kai akalla tan miliyan 5.26, a takaice dai ana faduwa da kusan tan miliyan 4.5. Ya ce, tazarar da ake samu tana da yawa sosai, don haka akwai bukatar saka hannun jari mai yawan gaske a bangaren noman alkama domin bunkasa fannin noma.
Ministan wanda ya samu wakilcin Darakta a ma’aikatar, Hajiya Karima Babangida, ya jinjina wa Shugaba Buhari bisa kokarinsa na bunkasa fannin noma da mayar da fannin akalar bunkasa tattalin arziki. Ya kuma yaba wa CBN da Kungiyar Kamfanonin Fulawa ta Najeriya (FMAN).
A nasa jawabin, Kwamishinan Noma kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Nasiru Gawuna, ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya bisa ba wa bangaren noma muhimmanci. Rahotan aminiya