Mun kashe Naira biliyan 40 wajen ciyar da ‘yan gudun hijira – Zulum
“Babu wata jiha a Najeriya da gwamnati ke kula da bukatun ‘yan gudun hijira na tsawon shekaru kamar jihar Borno.”
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe sama da Naira biliyan 40 wajen biyan bukatun mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a cikin shekara guda da ta wuce.
Mista Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ‘yan gudun hijira a Mafa, mahaifarsa ranar Lahadi.
Da yake mayar da martani kan rade-radin da wasu bata gari ke yi a garin Dikwa da Mafa na cewa ‘yan gudun hijirar sun yi barazanar komawa dazuzzukan da aka ceto su daga hannun mayakan Boko Haram saboda tabarbarewar tattalin arziki, gwamnan ya ce lamarin wata matsala ce ta duniya da yakin Rasha da Ukraine ke haifarwa.
Mista Zulum ya ce ‘yan gudun hijirar na bukatar godiya ga gwamnatin Borno a daidai lokacin da ake daukar matakan da suka dace domin tallafa musu.
“Babu wata jiha a Najeriya da gwamnati ta kwashe shekaru tana kula da bukatun ‘yan gudun hijira kamar jihar Borno,” in ji shi.
Mista Zulum ya yabawa Gwamnatin Tarayya, Sojoji, Jami’an tsaro da kuma ‘yan sa kai bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen inganta harkar tsaro da ya kai ga sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu a jihar.
Gwamnan, wanda ya bayyana cewa kashi 90 cikin 100 na mutanen da aka sake tsugunar da su za su iya shiga gonakinsu, ya kuma umarce su da su shiga aikin noma maimakon jiran abin da ba zai dore ba.
Gwamnatin jihar Borno ta yi nasarar tsugunar da mutane biyu cikin miliyan uku da aka yi kiyasin ‘yan gudun hijira a jihar.
(NAN)