Mun kashe Sama da milyan dari tara 920m domin yaki da corona- Gwamna masari
Gwamnatin jihar Katsina ta kashe kasa N920m domin yaki da cutar Corona tun daga farkon zuwan cutar a cikin jihar. Gwamnatin jihar ta kuma karɓi gudummawar daga al’umma har kimanin N700m daga masu ba da agaji da kuma masu kyakkyawar niyya ta mutanen jihar Katsina
Wannan jawabin nasa Shugaban kwamitin ba da amsa na gaggawa na COVID-19, QS Mannir Yakubu ya Jagoranci Gwamnan Jihar Katsina yayin bikin raba kayan tallafi ga mutane masu rauni a cikin jihar wanda Coalition Against COVID- ta bayar.
(CACOVID). QS Mannir Yakubu ya kuma nuna cewa jihar zuwa yanzu sama da mutun 746 ne suka warke yayinda 24. suka mutu Sakamakon Cutar
Yakubu, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar, na musamman ya kara da cewa, ya zuwa yanzu an sallami marasa lafiya 705, yayin da marasa lafiya 17 ke karbar magani, gwamna Aminu Bello Masari, wanda ya bayarda damar rarraba kayayyakin a ranar Laraba, ya ce kayan za su bayar da taimakon da ya dace ga mawuyacin halin da gidaje ke ciki a fadin jihar. Ya yi bayanin cewa, gidaje 67,106 da suka fi fama da cutar an sanya su ne don cin gajiyar tallafin ayyukan agaji da CACOVID ya bayar. A cewar gwamnan, kowane Magidanci zai sami 10kg na shinkafa, masara, 5kg na sukari, kwali biyu na taliya da 1kg na gishiri a jere.