Mun kori marafa daga Jam’iyar APC da jumawa.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara ta ce har yanzu tana nanata cewa Sanata Garba Kabiru Marafa haryanzu ba mamba din APC bane, yana mai cewa jam’iyyar ta kore shi tun daga 2019. Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Lawal Liman ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani game da kwanan nan bayanan da Sanatan ya nuna zarginsa ga Kwamitin riko na kasa na jam’iyyar karkashin jagorancin Buni MaiMalam Gwamnan yobe
Jam’iyyar tace tun daga shekarar 2019 mun dakatar da shi ne bisa tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar kuma shawarar da muka yanke an tura zuwa Hedikwatar APC ta Kasa, Abuja”
Ya bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, comrade Adams Oshemole ya bashi kariya shi kariy ba bisa ka’ida ba saboda suna raba fa’idar APC ta fadi a zamfara.
“Saboda haka, ya kamata jama’a su yi watsi da shi a matsayin memba na All Progressive Congress (APC)”
“Ba mu dauki Marafa a matsayin membanmu ba tunda jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) tana amfani da shi don karkatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar musamman APC a jihar Zamfara”
A cewarsa, ta hanyar rashin biyayya ga Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC) ya kamata ya zama isasshen dalili a san cewa Marafa ba ya fatan APC ta yi kyau “, Liman
“Muna kira ga kwamitin riko na kasa da ya dauki tsauraran matakai a kansa, saboda haka ya kamata a dauke shi a matsayin dan adawa.
“Saboda haka, mun yi tir da kalaman, mun nisanta kanmu daga duk wani kira ga Shugabancin jam’iyyar na kasa”, in ji Liman.
Ya lura cewa jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara na matukar goyon bayan Shugabancin jam’iyyar na kasa, “muna yaba wa kwamitin Maimala Buni saboda sake kafa jam’iyyar”.
Jaridar Vanguard ta Najeriya