Labarai

Mun kusa Samar da aiki ga ‘yan Nageriya mutu dubu Dari biyar 500,000 a masana’antar karafa ~Cewar Shugaba Tinubu.

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa a yanzu haka an kusa kammala aikin ginin karafa na Ajaokuta da aka yi watsi da shi, aikin zai samu karfin daukar ‘yan Nijeriya aiki har mutun 500,000 da zarar an hada Hadar kaduwancin sa.

Shugaban ya kuma yi alkawarin yin cikakken amfani da wannan katafaren ginin da zarar an kammala shi, domin zai bunkasa zuba jarin Najeriya kai tsaye da kuma samar da hanyoyin samar da ingantaccen yanayin kasuwanci da ake bukata domin kowane bangare ya samu ci gaba.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasar, ya bayyana haka a wajen kaddamar da yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a Lokoja, babban birnin jihar Kogi na zaben gwamna da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button