Mun raba tallafin dubu ashirin ashirin ga Matan karkara a jihohi goma sha shida na Najeriya, in ji Minista Sadiya.
Matan Fulani 247 ne suka samu tallafin FG’s Rural Women Cash a Kebbi.
Kimanin matan Fulanin 247 karkashin inuwar kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, a jihar Kebbi za su karbi N20,000 kowannensu don inganta tattalin arzikinsu.
Ministar kula da ayyukan jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Sadiya Umar-Farouq ce ta bayyana hakan a lokacin da ta kaddamar da tallafin kudi na musamman na Gwamnatin Tarayya don matan karkara a matsugunin Fulani da ke Hutawa kusa da Birnin Kebbi.
Mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yada labarai, Nneka Ikem Anibeze, a cikin wata sanarwa, ta ce “Ministan wanda ya ziyarci Mazaunin Fulani da ke wajen garin Birnin kebbi a karshen mako ya nuna farin ciki kan horaswar karfafa tattalin arzikin da gwamnatin jihar ke baiwa matan Fulanin. ”
Sanarwar ta ambato ta tana cewa, “Na yi matukar farin cikin ganin cewa ana koyar da wadannan matan Fulani hanyoyin zamani na samar da yoghurt ta hanyar amfani da madarar shanu. Wannan zai taimaka kwarai da gaske wajen karfafa musu gwiwa don dogaro da kai da iya ciyar da iyalansu. ”
“Ina yi wa dukkan matan Fulanin da gwamnatin jihar Kebbi ta bawa wannan horo da su sanya ta a aikace saboda hakan kuma zai inganta matsayin tattalin arzikin ba na mata kadai ba har ma da jihar da ma kasa baki daya”, in ji ta.
Sanarwar ta ce, daga cikin wadanda suka samu wannan tallafi na Musamman na Gwamnatin Tarayya don Matan Karkara, sanarwar ta ce, “akwai Baba Hauwawu mai shekara 65 da ta kasa daurewa lokacin da take farin ciki lokacin da Minista Sadiya Umar Farouq ta gabatar mata da kudin.”
Ta nuna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari game da wannan tallafi sannan kuma ta ce za ta yi amfani da N20,000 wajen fara kasuwancin Fura.
”Allah ya saka da alheri ya kuma rike Baba Buhari bisa wannan kudin da ya bani. Yanzu zan je in sayi Fura sannan in fara kasuwancin kiwo ”, in ji ta.
“An fara bayar da tallafin kudi na musamman na Gwamnatin Tarayya ga matan karkara a jihohi 16 da suka hada da Plateau, Sokoto, Imo, Ebonyi, Nassarawa, Kebbi, Katsina, Bauchi, Taraba, Ekiti, Ondo, Adamawa, Gombe, Kano, Jigawa da Zamfara jihohi, ”in ji sanarwar.