Labarai
Mun riga da gama da batun Atiku – Shugaban kasa
Fadar shugaban kasa, ta ce babu bukatar a girmama tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar tare da mayar da martani kan harin da ya kaiwa gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Da yake mayar da martani kan kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa na baya-bayan nan inda ya shawarci shugaba Tinubu da ya manta da batun 2027 da za a yi zabe ya mai da hankali kan gudanar da mulki.
fadar shugaban kasa ta bakin mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama’a, Sunday Dare, ta ce abin da Gwamnati Tinubu tafi mayar da hankali shine yadda za ta kawo taimako da Ci gaba ga jama’ar Nageriya.