Rahotanni

Mun shirya tsaf don sake zaben gobe Asabar – INEC

Spread the love

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta raba kayan zaben da za a sake gudanarwa a ranar Asabar a kananan hukumomi shida na jihar Zamfara.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ta raba kayan zaben da za a sake gudanarwa a ranar Asabar a kananan hukumomi shida na jihar Zamfara.

Kwamishinan zabe na jihar Zamfara, Saidu Ahmad ne ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis a Gusau.

Ya ce zaben dan majalisar dattawan Zamfara ta tsakiya ne da kujerun majalisar wakilai biyu na mazabar tarayya ta Gusau/Tsafe da Gummi/Bukkuyum.

Mista Ahmad ya ce za a sake gudanar da zaben Sanata a kananan hukumomin Gusau, Maru, Bungudu, Gummi, Tsafe da Bukkuyum.

Kwamishinan zaben ya bayyana cewa za a gudanar da zaben ne a rumfunan zabe 90 a yankunan rajista 24 na kananan hukumomi shida.

A cewarsa, rumfunan zabe 90 na da masu rajista 95,332, inda 90,900 suka karbi katin zabe na dindindin.

Malam Ahmad ya yi kira ga ‘yan siyasa da ‘yan jarida da su kara wa masu zabe kwarin guiwa da su fito su kada kuri’unsu a kan lokaci domin kammala aikin a lokacin da ya dace.

Kwamishinan zaben na Zamfara ya kara da cewa, hukumomin tsaro sun tabbatar wa INEC cewa za su bayar da kariya ga masu kada kuri’a domin gudanar da zabensu cikin lumana.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button