Kungiyoyi

Muna farin ciki da yajin aikin kai kayan abinci yankin kudu da ‘yan kasuwarmu sukayi – Arewa Media Writters.

Spread the love

Kungiyar Masu Kayan Abinci Na Arewa, Sun Shiga Yajin Aikin Kai Kayan Abinci Yankin Kudu

…Kungiyar “Arewa Media Writers” tana farin ciki da hakan, tare da kara jaddada goyon bayanta.

Hadaddiyar kungiyar kayan abinci na kasa ta shiga yajin aikin kai abinci yankin kudancin Kasar har sai baba ta gani.

Kungiyar za ta fara tare duk wata hanya na kayan abinci, kama daga kayan gwari, shanu, awaki da duk wani nau’in nama, ko hatsi masara, dawa, shinkafa, da duk wani kayan abinci da zai bi ya wuce zuwa kudancin Nijeriya.

Kungiyar ta shiga yajin aikin ne sakamakon irin barnatar da dukiyan al’ummar Arewacin kasar nan da ‘yan kudancin Nijeriya suke yi, a duk lokacin da suka ga dama, inda suke kona motocin kayan abinci su kashe ‘yan Arewa tare da kona shagunan ‘yan arewa. Kuma babu wani mataki da aka dauka.

Da wannan dalilin ne Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, tana farin ciki da hakan, tare da kara jaddada goyon bayanta kan dakatar dakai abinci kudancin Kasar, har sai gwamnatin kasar ta dauki mataki kan kisan da ake yiwa ‘yan Arewa a kudancin Kasar.

Haka zalika kungiyar “Arewa Media Writers” tana kira da kakkausan harshe ga duk wanda yasan shi cikakken dan Arewa ne, mai kishin al’ummar Arewa da ya bada tashi gudummuwar a ko’ina yake, don ganin an dakatar da shigar da duk wani abu zuwa yankin kudancin Kasar, har sai gwamnatin kasar ta dauki mataki kan cin kashin da suke yi mana a yankunan su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button