Labarai

Muna godiya ga Allah domin Kotu ta tabbatar da muradin Al’ummar jihar Zamfara ~Gwamna Dauda

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana tabbatar da nasarar da ya samu a zaben a matsayin tabbatar da muradin al’ummar jihar Zamfara.

Gwamna Dauda Lawal ya yi nasara a zaben Gwamna da aka yi a watan Maris inda ya doke mai ci da gagarumin nasara.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwa da ya fitar a yau ranar Litinin a Gusau, ya jaddada cewa hukuncin kotun yana wakiltar ra’ayi da shawarar mutanen jihar Zamfara.

Ya ce: “Dan kadan da suka gabata ne kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Zamfara da ke zamanta a Sakkwato ta tabbatar da Dauda Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a ranar 18 ga Maris, 2023.

“Hukuncin ba abin mamaki ba ne, illa dai tabbatar da hukuncin gamayya ne da al’ummar Zamfara suka yanke.

“Gwamna Dauda Lawal ya yi nasara a zaben gwamna da tazarar kuri’u 65,750.

“A sani cewa wannan nasara ta dukkan al’ummar Zamfara ce ba Gwamna da jam’iyyarsa kadai ba.

“Hukuncin zai karfafa wa Gwamna Lawal kwarin gwiwar ci gaba da kudurinsa na cika aikin sa da kuma yin aiki tukuru domin ganin al’ummar Jihar Zamfara sun samu nasarar gudanar da shugabanci nagari.

“Aikin ceto Gwamna Dauda Lawal wanda aka fara tun a ranar 29 ga watan Mayu bayan rantsar da gwamnatinsa, tuni ya samu gagarumin ci gaba wajen inganta tsaro, ilimi, ababen more rayuwa, da noma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button