Muna Jinjina ga Ganduje daya kawo Mana karshen masifa a jihar Kano ~Inji Sheikh Qarubullah Nasiru kabara.
A wani bidiyon Dake yawo an hango Shugaban darikar qadiriyya na Africa Sheikh Qarubullah Nasiru kabara yana Mai Jinjinawa Gwamna Ganduje bisa matakin daya dauka na dakatar da karatun Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara a lot Wacce Makarantarsa Dake Jihar kano a Cikin Kalaman Sheikh Qarubullah Yana Cewa muna godiya tare da Jinjina ga Mai girma Gwamnan Jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa matakin daya fara dauka a matakin Farko Kan Wannan masifa data addabi jihar kano..
Hakika wannan Abin a yaba Masa ne Kuma muna goyon bayan Muna tare dashi zamu bashi gudunmawar addu’a Kan Wannan masifa dukda Shehun malamin Bai ambaci sunan ba Amma dai Kalaman nasa bashi rasa nasa ba da dakatarwa da Ganduje yayima Malam Abdujabbar…
Tsakanin Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara da Sheikh Qarubullah Nasiru kabara dai an juma ana rigima dukda Cewa mahaifin su Daya…