Muna Rokon Gwamnati Ta Bude Mana Makarantu- ASOF.
Kungiyar wayar da kan dalibai ta arewacin Najeriya {Arewa students orientation forum} ta roki Gwamnatin tarayya da na Jahohi da su taimaka su bude makarantu.
A tabakin shugaban sashin shirye shiryenta Comr. Umair Kabir yace, kullum dalibai na nuna rashin jin dadinsu game da Al’amarin rufe makarantu da gwamnati tayi sabida cutar covid-19, haka kuma a kullum muna samun sakonni daga dalibai sama da dari biyu akan rokon gwamnati data bude makarantu.
Ya kara da cewa “munyi farin ciki da jin matakin da hukumar ilimi ta dauka akan bada wa’adin da kowanne makarantu zasu cika sharudan data gindaya domin bude makarantu”.
Sannan muna rokon gwamnati da ASUU dasu daidaita akan al’amarin IPPS , sannan ASUU tayi duba akan sharudan data gindayawa gwamnati akan bude makarantu, sabida anan kusa mun san gwamnati bazata iya cikasu ba, sabida matsalolin da suke gabanta.
Idan muka rasa wannan shekarar al:amuran karatu da dama zasu dawo baya.
25/07/2020
Shehu Rahinat Na’Allah