Labarai

Mune muka sace daliban Makarantar kankara ta Jihar katsina ~Inji Shekau

Spread the love

Shugaban bangaren kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya dauki alhakin sace daliban Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kankara, jihar Katsina.

Shekau, a cikin wani sakon sauti da HumAngle ya fara bugawa ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne don ‘bunkasa addinin Musulunci da kuma hana ayyukan da ba na Musulunci ba’.
Abin da ya faru a Katsina an yi shi ne don ciyar da addinin Musulunci gaba da kuma hana ayyukan da ba su dace da Musulunci ba kasancewar ilimin Yammaci ba irin karatun da Allah da Annabinsa suka yarda ba ne, ”inji shi.
Ba sa kuma koyar da abin da Allah da AnnabinSa suka yi umarni. Sun gwammace su rusa addinin Musuluncin. amma Allah Ubangijin sama da kasa ya san abin da yake boye. Allah Ya daukaka Musulunci mu mutu muna Musulmi. ”

“A takaice, muna bayan abin da ya faru a Katsina,” in ji shi.

Akwai alkaluma da ke karo da juna dangane da ainihin adadin daliban da aka tafi da su amma gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na tattaunawa da wadanda suka sace daliban da suka bata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button