Murnar 60 Shugaba Buhari da El’rufa’i na neman goyon bayan ‘yan Nageriya~ Sanata Uba Sani
Bikin murnar Shekaru sittin 60 da samun ‘yancin Nageriya Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya Yace ina jinjina tare da girmama ‘yan uwanmu ‘yan Nageriya a wannan lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai. lallai Tamu tafiya ce ta nasara tare da Rashin Samun wata damar Kuma da ƙalubale muna da juriya mun shawo kan matsaloli da yawa kuma mun kasance kan turbar ci gaba mai dorewa.Kakanninmu da suka kafa tubalin suna da burin samun ci gaban Nijeriya. Sun ba da gudummawar su kuma sun duba sabon ƙarni don ƙarfafa abubuwan da suka samuSun bamu samfuri hanyoyin bi ta cikin mawuyacin yanayin ƙasar Nijeriya. Amma Mun kasa riko da ɗabi’un da suka gadar mana.
juriya da addini ya sa yawancin al’ummominmu da kyar ake rungumar shugabanci a matsayin aiki Da wuya mu sanya mutane a cibiyar ci gaba sai muka shagala da Kayan alatu Tambayar mutane da yawa ita ce ta yaya muka sami wannan rashin haƙuri haka? Amma fata ba a rasa ba. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dukufa wajen nadin sabon tsarin mulkin kasa na aminci a cikin aikinsa. Ya kuduri aniyar kawar da cin hanci da rashawa wanda hakan ya saba donin sauke hakkin Al’ummar sa Shugaban kasar da tawagarsa suna aiki kafada da kafada don tabbatar da cewa tattalin arzikinmu ya tsira daga kalubalen annobar COVID-19 ta assasa.
An fitar da kayan kara kuzari don rage tasirin cutar ga talakawa da marasa karfi da ‘yan Najeriya Baki daya, musaman kan kasuwancinsu. Gwamnatin Buhari na bukatar cikakken goyon bayan mu yayin da take fama da kalubalen sarrafa tattalin arziki a wannan lokacin na COVID-19.
Masoyinmu, Malam Nasir El-Rufai yana kan gaba gaba Kan kokari na wadannan mawuyacin lokaci. Bai yi Sanya ba da Bata lokaci ba cikin neman hanyar ci gaba da yakin. Cibiyoyi masu mahimmanci kamar ilimi, kiwon lafiya da noma suna samun cikakken kulawa. Ya kasance yana aiki tare da masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro don shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna. Dole ne mu tsaya tare a bayan Gwamnan mu domin dawo da jihar Kaduna kan turbar zaman lafiya da ci gaba. A wannan lokaci mai albarka,
Har’ila yau a daidai wannan lokaci ina jinjina wa ya mazabata, manyan mutanen kirki a gundumar Sanatan Kaduna ta Tsakiya nayi iya kokarina na cika yarjejeniyar a tsakaninmu bisa alkawarin dana dauka na dauki nauyin Kudiri (Bill) masu tasiri kuma na Kai su majalisar dattijai Na amsa kiran gaggawa daga mazabata. Na yi ƙoƙari don rage matsalolin da radadi da mutanena suka fuskanta a lokacin da akayi kullen COVID-19.Na shiga cikin harkokin kiwon lafiya, ilimi da noma. Na yi aiki da Gwamnatin Jiha da hukumomin tsaro kan dabarun da za a bi don magance karuwar matsalar rashin tsaro a wasu sassan mazabunmu. Haka Zalika zan fara kirkirar wasu Sabbin Kudirin na Bill wadanda za su taimaka wajen karfafa mutanenmu da sake sanya yankin a sahun fuskar tattalin arziki.Mutanenmu sun cancanci taimako domin Sun riƙe imanin su a tare da ni. Ba zan huta ba kan bakana ba har sai mazabun mu sun zama abin koyi ga kowa.
A yayin da muke bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai, ina kira ga‘ yan kasarmu maza da matanmu da su ci gaba da kasancewa cikin tsammanin cewa Kalubale da matsalolinmu yanzu zasu kasance kyakkyawar hanya ga Najeriya. Dole ne mu rungumi zaman lafiya tare da marawa shugabannin mu baya domin samun ci gaba.
Murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai Sanata Uba Sani (Kaduna ta Tsakiya)