Labarai

Murnar Zagayowar Ranar haihuwa Sanata Uba Sani ya Tallafawa Marayu Mutun dari takwas 800.

Spread the love

Dangane da bin ka’idojin kare lafiya na cutar Covid-19, Sanata Uba Sani, mai wakiltar gundumar Kaduna ta Tsakiya a Lokacin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 50 ya Tallafa ta hanyar sanya murmushi da Farin Ciki a fuskokin marayu mutun dari takwas 800 a gidajen marayu hudu Dake fadin mazabarsa.

Taimakon wanda aka shimfida shi ta hanyar aikin gidauniyar ta Sanatan wanda aka fi sani da Uba Sani Foundation, gidauniyar ta isa ga marayun sama da 800 a gidan marayu na Ummu Atyam Unguwan Dosa da Gidajen Marayu na Addonai, Barnawa sa Gidan Marayu Naphtali, Gonin Gora; da Gidan Marayu na Al-Ihsan Dake Nasarawa.

Uba Sani wanda ya yi magana ta bakin Ibrahim Dan-Halilu, Daraktan Gidauniyar Uba Sani a yayin taron ya ce yanayin da ya dace na yin bikin maulidin ya kara wa sanatan kwadayin taimakon jama’a yayin da Kuma yake yin babbar nasara a majalisar dokokin ta tarayyar inda Sanata ya Mai da Hankalin Kan kudrai BILL na makarantu da sauransu domin cigaban Al’ummarsa.

Dan-Halilu ya ci gaba da cewa Sanatan ya zabi yin bikin maulidin nasa ne a cikin nutsuwa yadda ya dace da yanayin al’ummar kasar da kuma bin ka’idoji sharudan cutar COVID-19.

Uba Sani ya lura cewa a cikin wadannan kalubale da mawuyacin lokaci sanya murmushi a fuskokin marasa galihu, masu karamin karfi na sassan al’umma ya zama muhimmin abu na gaggawa: “Ba za mu iya da’awar cewa muna kaunar Allah ba alhali ba za mu iya rage radadin masu bukatu ba.

Gidauniyar ta Sanatan dai ta rarraba kayayyakin abinci daban-daban, kayan wanka, barguna da sauran kayayyaki ga duk gidajen da aka ziyarta yayin da shugabannin gidajen marayu daban-daban da aka ziyarta suka yaba wa Sanata Uba Sani bisa kyakkyawar niyyarsa yayin da suke yi masa addu’ar samun nasara a Majalisar Dattawa da kuma sauran abubuwan da ya sa a gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button