Rahotanni

Musulma Ilham Omar Ta Sake lashe Zaben ‘yar Majalisa a Amurka.

Spread the love

Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press a kasar Amurka ya ruwaito cewa Yar majalisar wakilai Ilhan Omar ta sake lashe zabe a kan abokin karawarta na Jam’iyar Republican Lacy Johnson a gundumar majalisa ta biyar da ke Minnesota.

Omar ta lashe gundumar, wanda ya hada da kananan hukumomin Anoka, Hennepin da Ramsey, jim kadan bayan kammala zaben. AP ta bayyana sakamakon ne da misalin karfe 8:45 na dare. A daren Talata Ilham Omar ta sami sama da kashi 64 na kuri’un Yayinda Johnson ya samu 25 Cikin kashi 100 na wuraren da aka ba da rahoto a daren Talata.

Gundumar majalisa ta biyar itace amintacciyar majalisar ta DFL, kasancewar ‘yan Democrats ne ke rike da ita tun daga 1963. Zuwa shekarar 2018, Omar ta doke dan takarar Republican Jen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button