Labarai

Mutane 10 Sun Mutu A Wani Hatsarin Kwale-kwale A Jihar Neja.

Spread the love

Akalla mutane 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hatsarin kwale-kwale, wanda ya faru a Kogin Shiroro na jihar Neja da yammacin ranar Laraba.

An gano gawarwakin biyu daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su yayin da ba a gano wasu mutum bakwai ba.

Wannan lamari na baya-bayan nan na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da mutane biyar suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa, yayin da suke kokarin tserewa daga hannun ‘yan bindiga a garin Gurmana a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

An rawaito cewa hatsarin na ranar Laraba ya faru ne lokacin da wadanda lamarin ya rutsa da su ke dawowa daga gonakin su a kauyen Kudumi bayan sun girbe wasu kayan amfanin gonar su.

Shaidun gani da ido sun ce kimanin mutane 19 ne ke cikin kwale-kwalen, wanda shi ma ke dauke da buhuna da yawa na sabuwar shinkafar da aka girbe a cikin kwale kwalen.

A cewar rahoton manoman sun shiga cikin yanayi na hadari, wanda hakan ya sa jirgin ruwan ya kife.

An ce masu ceto sun garzaya don ceto ‘yan manoman amma bakwai daga cikinsu ne aka fitar da rai.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Alhaji Ibrahim Ahmed Inga lokacin da aka tuntube shi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Inda ya ce an binne gawar wadanda suka mutu yayin da za a ci gaba da neman sauran.

Ya tausayawa dangin wadanda suka mutu ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button