Mutane 15 Ne Suka Jikkata A Harin Da Aka Kaiwa Gwamna Zulum.
A kalla mutane goma sha biyar sun ji rauni a ranar Laraba yayin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai hari kan ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
Gwamnan ya zagaya wasu kananan hukumomi a arewacin Borno don tabbatar da kare lafiyar wadanda suka dawo daga yankin tare da samar da wadata ga wadanda rikicin ya ritsa da su.
Gwamnan da mukarrabansa sun kasance a garin Baga, daya daga cikin wuraren da ke da wahala ga ayyukan jin kai, a lokacin da kungiyar ta’adda ta yi wa ayarin sa kwanton bauna.
Jami’an tsaron dake kare lafiyar gwamnan sun mayar da harin, amma ba tare da jikkata ba a bangaren sa.
Gwamnan yana kan hanyarsa don rarraba kayan agaji ga ‘Yan gudun hijirar cikin karamar Hukumar Monguno bayan barin garin Baga lokacin da lamarin ya faru.
Ya yi sa’a ya tsere daga harin ba tare da wata matsala ba, sannan ya ci gaba da tafiyarsa don rarraba kayan agaji.
Wata majiya ta fada wa DAILY POST, cewa wannan shi ne karo na uku da ‘yan ta’adda suka kaiwa ayarin gwamna hari.