Labarai

Mutane Dubu 16 Na Neman EFCC Ta Binciki Bola Tinubu Kan Motar Kudi Da Aka Gani A Gidansa.

Spread the love

Akalla ‘yan Najeriya Dubu 16 ne suka sakawa wani kira na a binciki jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu kan motar kudi da aka gani a gidansa.

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omokri ne ya fara wannan kira a shafin Change.org inda yace ya kamata ‘yan Najeriya su tashi tsaye su kwatarwa kansu ‘yanci kada komai aka yi suce kauda kai.

An ga motocin kudinne a gidan Tinubu a shekara 2019 yayin da ake shirin zaben shugaban kasa. Saidai da aka tambayeshi akan hakan yace shi ba ma’aikacin gwamnati bane kuma bai taba karbar kwangila daga gwamnatin Buhari ba, kudinsa ne dan haka a daina saka masa ido.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button