Mutane Guda 500 Suna Neman Hana El-Rufa’i Zuwa Wani Muhimmin Taro.
Akalla mutane 500 ne suka saka hannu a wani kira na hana gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai halartar taron kungiyar Lauyoyi ta kasa, NBA da ake yi duk shekara.
Gangamin da aka farashi ta shafin Change.org ya samu kulawar mutane da dama awanni kadan da farashi. Mun ruwaito muku cewa hakan na faruwane saboda kalaman da gwamnan yayi a gidan talabijin din Channelstv akan mutanen kudancin Kaduna wanda baiwa wasu dadi ba.
Kiran yayi bayanin cewa gwamnan Kadunan yawa lamarin rikon sakainar kashi wanda kuma duk da su lauyoyin babu wani mataki da zasu iya dauka akai to amma zasu iya hanashi halartar tason su dan nuna rashin jin dadinsu kan lamarin.
Gagamin yayi kira da cewa maimakon gwamna El-Rufai, kamata yayi a gayyaci gwamna Zulum wanda yafi El-Rufai nagarta.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe.