Mutane ne ke son batawa Abdul’aziz Yari suna, tun A 1999 yake kasuwanci kafin Shiga Siyasa.
Mutane yakamata ku tambayi kanku tun kafin kotu ta yanke hukunci shi wai nawane ake zargin Tsohon Gwamna Yari ya mallaka ba bisa Ka’ida ba ? Masu karatu yakamata kun yake hukunci.
‘Yan Furofaganda ne kawai suke yayata shari’ar da ake yi game da batun adana kudade a bankunan Zenith da Polaris Banks na tsohon Gwamna Yari ba zaku taba yin nasarar rage masa martabar siyasarsa ba.
Makiyansa ne kawai na buƙatar yin aiki tare don kawai su bata masa siyasa kuma bazakui nasara ba
Tun kafin a gama yanke hukunci mutune na bukatar su tambayi kansu nawa ne kudin da ake zargin tsohon Gwamnan daya mallaka ba bisa ka’ida ba ?
Kafin dawo da mulkin dimokiradiyya a 1999, tsohon Gwamnan yana cikin kasuwancin sa na cikakken lokaci kuma daga baya ya kasance a tsakiyar harkar siyasa da ta kawo Ahmed Sani (Yarima) kan karagar mulki a shekarar 1999. Gwamna Yari yakai tsawon shekaru 25 ba tare da kasawa ba. Da irin nasarorin dayayi a kasuwanci da kuma siyasa.
Ana kokarin gurfanar da tsohon Gwamnan kan kudin da bai gaza N278,989,960 ba wanda ya isa ya sanya makiyansa izgili da dariya. Su rufe kawunansu cikin jin kunya su nemi gafarar Allah (SWT).
Gaskiyar magana ita ce, har yanzu shari’ar tana nan kuma da yardar Allah gaskiya za ta yi halinta, Mai girma Abdulaziz Yari Abubakar zai kunyata makiyansa a idon duniya, Daga Aliyu Adamu tsiga