Mutane Sun Yi Caa Akan Hadimin Shugaban Kasa, Bashir Ahmad Saboda Yace Yana Goyon Bayan Hukuncin Kisa Kan Wanda Yayi Batanci Ga Annabi.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Bayan da kotu shari’ar musulunci a Kano ta yankewa wani matashi, Yahaya Aminu Sharifai hukuncin kisa saboda samunshi da laifin kalaman batanci ga Annabi(SAW) lamarin ya jawo cece-kuce.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama musamman daga kudancin Najeriya sun fara fitowa suna kare matashin. A jiyane dai, Muka kawo muku yanda kotun ta yankewa matashin hukunci
Saidai wannan hukunci ya jawo yanda wasu suka koma baya suka zakulo wata magana da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya taba yi a shafinsa na Twitter,kamar yanda hutudole ya samo ya rubuta cewa yana goyon bayan hukuncin kisa akan wanda yayi batanci tun shekarar 2015.
Da yawa dai musamman wanda ba Musul.i ba kuma daga kudancin Najeriya sun yi Allah wadai da wannan kalami nashininda suke ganin hukuncin yayi tsauri.