Labarai
Mutanen Da Suke Zargina Da Sata Suna Yi Ne Kawai Don Su A Tunaninsu Kowa Ma Barawo Ne Kamarsu~ Atiku Abubakar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan Takarar Shugancin Kasa Na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya yi zazzafan martani ga wadanda suke yi masa kallon barawo.
Ya ce “‘Yan Najeriya suna ganin babu yadda za ayi mutum yayi kudi ba tare da yayi sata ba, abin na damuna, yadda ake yayata zargin rashawa akaina, bayan mutanen dake wannan zargin duk sun kasa kawo wata hujja kwakwkwara akaina.”
“Mutanen da duk suke zargina da sata, sunayi ne kawai domin su a tunanin su kowa ma barawo ne kamar su.”
“Idan kuma sunce Atiku Abubakar barawo ne saboda nasarorin daya samu a rayuwa, to ‘yan adawata masu fadar haka su fada mini Inda suka sami nasu kudin.”
Inji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.
Daga Kabiru Ado Muhd.