Mutum daya ya mutu yayin arangamar Yarbawa da Hausawa a Ibadan.
Akalla mutum guda aka ruwaito ya mutu, yayin da Hausawa da Yarbawa suka yi arangama a Shasha da ke karamar Hukumar Akinyele a Jihar Oyo ranar Juma’a.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa rikicin ya fara ne a lokacin da wani bahaushe ya bada labarin cewa ya yiwa wata mata mai juna biyu duka wanda ya zarge ta da yin lalata a gaban shagonta, yayin da mutumin da ya mutu, wani dan farar hula da ake kira Adex ya shiga tsakani amma ya gamu da ajalinsa kamar yadda bahaushe ya ce ya buge shi da tsafi.
A cewar shaidun gani da ido, Adex ya fadi nan take ya fara kumfa a baki kafin a garzaya da shi wani asibiti da ke kusa da shi inda rai yayi halinsa da safiyar yau.
A halin da ake ciki, an hada wasu tawaga na Amotekun da Operation Burst zuwa yankin amma har yanzu al’amuran sun dawo kamar yadda kone-kone da barnata dukiya ke ci gaba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.