Labarai

Mutun dubu 46,732 ne ke dauke da cutar kanjamau a jihar Kano yayinda mutun dubu 4,728 suka kamu a wannan shekara ta 2023.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta ce akalla mutane 4,728 ne suka kamu da cutar kanjamau a shekarar 2023 a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya na bana mai taken ‘Bari Al’umma su jagoranci.

A cewarsa, jimillar mutane 46,732 ne ke dauke da cutar kuma suna karbar magani a jihar.

Ya ci gaba da bayyana cewar jihar ta inganta dabarunta na dakile yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa ’ya’ya ta hanyar yin nasarar gudanar da gwajin kashi 95 na dukkan mata masu juna biyu a ziyarar da suka kai na farko wajen haihuwa, inda kashi 0.04 ne kawai aka samu.

“Mun gwada jimillar mutane 138,430 ko suna dauke da cutar kanjamau kuma mun gano 4,728 sun kamu kuma mun samu nasarar fara sabbin masu dauke da cutar kanjamau 4,140 a ART daga watan Janairun 2023 zuwa yau.

“A halin yanzu jihar na da mutane 46,732 da ke dauke da cutar kanjamau suna karbar magani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button