Labarai

Mutun Milyan ashirin 20 zasu talauce a karkashin mulkin Buhari ~Bankin duniya

Daraktan bankin dake kula da Najeriya Shubham Chauduri yace Najeriya na cikin tsaka mai wuya a tarihinta, kuma yanzu ne lokacin da ya dace gwamnati ta dauki kwararan matakai masu tsauri wajen kaucewa yadda aka saba tafiyar da kasar domin rugumar sabbin hanyoyin gina kasa.

Shubham yace lokaci yayi da za a sauya fasalin tafiyar da tattling arzikin Najeriya da kuma amfani da sabbin dabarun da zasu taimakawa masu kananan masana’antu da kuma bangaren noma da samar da ayyukan yi.

Marco Hernandez, jami’in bankin dake kula da tattalin arziki yace Najeriya na iya fitar da kanta daga wannan matsala wajen baiwa ‘yan kasuwa damar taka rawa da samar da yanayi mai kyau da za’a samarwa matasa ayyukan yi.

Jami’in ya kuma bukaci karkata kudaden da ake bayarwa da sunan tallafin da attajirai ke mora zuwa matasa da kuma sanya harsashin bunkasa tattalin arzikin da zai fitar da mutane sama da miliyan 100 daga talauci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button