Labarai
Mutun takwas sun mutu ya yinda akayi Asarar dukiyar milyan 21.6m a jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce mutane takwas ne suka mutu tare da lalata dukiyoyin N21,650,000 a wasu gobara a watan Oktoba, 2023 a jihar.
Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce rundunar ta samu kiraye-kirayen kashe gobara guda 43, kirar ceto 21 da kuma kiran karya 10 a cibiyoyin kashe gobara 29 da ke fadin jihar a cikin watan da aka fara tantancewa.
Ya ce, “Kimanin dukiyar da bala’in gobara ya lalata ya kai na Naira miliyan 21,650, kiyasin dukiyar da mutanen mu suka ceto daga bala’o’in sun kai Naira miliyan 46,700,000, yayin da aka yi asarar rayuka takwas daga masifun na wuri daban-daban.
Adadin wadanda abin ya shafa da muka yi nasarar ceto da ransu daga bala’o’in gobara daban-daban sun kai 20.”