Labarai

Na baku awanni 12 Domin ku dawo da kayan Tallafin COVID-19 da kuka sace, duk gidan da na sami kayan sayar sai na Ruguje shi – Gwamnan Adamawa Ya Gargadi ‘yan jihar.

Spread the love

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bawa duk wadanda suka wawure kayayyakin tallafi na COVID-19 a rumbunan jihar sa’o’i 12 su dawo da su ko kuma su fuskanci mummunan sakamako.

Idan baku manta ba wasu gungun mutane sun afka wa wani sito a Yola, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, kuma sun wawushe dukkan kuyayyakin da ke ciki a ajiye.

A wata sanarwa da aka yi a duk fadin jihar a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, Gwamna Fintiri ya ce duk gidan da ya samu kayan sata zai ruguje.

Gwamna Fintiri ya ce: “Wannan wa’adin zai kare ne da karfe 6 na safe a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2020, bayan haka kuma zan sanya hannu kan umarnin zartarwa na neman gida-gida don farawa da karfe 7 na wannan ranar.

”Wani bangare na bayar da umarnin shi ne takunkumi wanda zai jawo janye C-of-O kuma idan ya cancanta, rusa kowane gida da ke dauke da duk wata kadara da aka sata.

“Ya kamata ‘yan ƙasa masu bin doka da haɗin kai ga hukumomin tsaro don tabbatar da yin hakan.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button