Na canza shawara, daga yanzu babu afuwa ga ‘yan Fashi da kuma ‘yan Boko Haram, in ji Shugaba Bihari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza shawara, ya ce daga yanzu babu afuwa ga ‘yan Bindiga da kuma ‘yan boko haram masu tayar kayar baya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce daga yanzu gwamnatin Sa ba za ta kara yiwa ‘yan bindiga da ‘yan boko haram masu tayar da kayar baya afuwa ba. Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin kawo karshen ‘yan Bindiga da sauran masu aikta laifin ta’addanci.
Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin bude taron hadin gwiwar tsaro na kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, majalisar gargajiyar Jihohin Arewa, da wakilai daga gwamnatin Tarayya, ya ce yanzu lokaci ya yi da za a dauki masu laifi a matsayin masu laifi.
Shugaba Buhari wanda yasamu wakilcin shugaban ma’aikatansa farfesa Ibrahim Gambari, ya ce kalubalen tsaro a kasar nan ya yi sanadiyar sanya ‘yan Najeriya cikin talauci da karayar tattalin arziki, don haka ya umarci shugabannin tsaro da su samar da sababbin tsare-tsare don kawo karshen ta’addanci a kasar.