Na fara Shirin Samarwa Matasa 774,000 Aiki Don Yaye Musu Takaicin Korona – Inji Shugaba Buhari.
Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Gwamnatinsa ta fara wani gagarimin shiri na gaggawar daukar matasa 774,000 aiki na musamman, domin yaye kuncin rayuwar da jama’a suka shiga sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus.
Da yake jawabi a ranar Juma’a yayin tunawa da Ranar Dimokradiyya, wadda ta koma 12 Ga Yuni, Buhari ya ce cutar Coronavirus ba karamar illa ta yi wa milyoyin jama’a ba.
“Da yawa sun rasa iyalai, ‘yan uwa da masoyan su. Wasu sun rasa aikin su baki daya. Milyoyi sun rasa dukiyoyin su. Tattalin arzikin wasu ya karye dalilin cutar Coronavirus.”
A kan haka ne Buhari ya ce gwannatin sa ta raba kayan tallafin rage radadin talauci da kuma raba bilyoyin kudade ga milyoyin marasa galihu a kasar nan.
Da ya juya a kan ayyukan musamman da ya ce gwamnatin sa za ta samar wa matasa kwanan nan, Buhari ya ce za a tsamo matasa 1,000 ne daga kowace karamar hukuma daga Kananan Hukumomi 774 da ake da su a fadin kasar nan.
Ya bada hakuri dangane da irin matsanancin halin kuncin da ‘yan Najeriya suka shiga, dalilin tsauraran matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin kokarin dakile cutar Coronavirus.
Ya ce cutar abin tsoro ce ganin yadda ta fara kamar da wasa a kasar China, amma ga shi cikin ‘yan watanni ta shafi mutum sama da milyan 7 a duniya a cikin kasashe 216.
Ya ce ko shakka babu Coronavirus babbar barazana ce ga rayuwar dan Adam gaba daya a duniya da kuma tattalin arzikin duniyar baki daya.
Idan ba a manta ba, Buhari ya rasa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari sanadiyyar cutar Coronavirus da ya dauko a kasar Jamus.
Kyari dai an yi ittifakin cewa a gwamnatance, shi ne mutumin da ya fi kowa kusanci da Buhari, kafin Coronavirus ta yi sanadiyyar ajalin sa.