Na Fidda Rai Ga INEC – Obaseki
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, a yau Asabar ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda zaben da ke gudana a yanzu haka da hukumar zabe mai zaman kanta, (INEC) ke yi a jihar.
Obaseki yayin da yake zantawa da manema labarai bayan jefa kuri’arsa a rumfar zabe 19, Ward 4, karamar hukumar Oredo, ya ce ya zauna na sama da awa daya da rabi a kan layin saboda mai karanta katin ya na jinkiri.
Gwamnan ya ce yana sa ran kyakkyawan tsari daga hukumar zaben.
“Na yi tsammanin cewa INEC za ta shirya sosai don wannan zaben.
Na jira awa daya da rabi a kan layi kafin na fara amfani da takardar izini, abin takaici ne. “Ganin cewa wannan zaben ne na yini guda, na yi tsammanin kyakkyawan shirin wannan zaben.
Masu karatun katin sun yi jinkiri sosai kuma wannan shi ne halin da ake ciki a ko’ina. “