Siyasa
Na Gama Shirin Barin Jam’iyyar PRP, Inji Takai.

Dan takarar gwamnan kano karkashin jam iyar ANPP da PRP babban na hannun daman tsohon gwamnan kano Malam Ibrahim shekarau, Malam Salihu Sagir takai yace ya gama shirin Sa tsaf don ficewa daga jam iyar PRP.
Sedai kawo yanzu Malam Salihu Sagir takai be bayyanawa manema Labarai jam iyar dayake shirin komawa ba.
Amma wani tsagi Na makusantan tsohon me Gidan Sa sunce ze komawa tsohon me Gidan nasa na farko ne.
A wani bangare na makusantan Malam Salihu Sagir takai din kuma sunyi hasashen cewa ze koma tafiyar tsohon gwamnan kano Alhaji Rabiu Musa kwankwaso ne.
Sedai yadda akaji daga Malam Salihu Sagir takai din dai.
Daga Kabiru Ado Muhd