Na Gano Gaskiya Jahilci Cuta ne babba akan marasa mutuncin dake tunanin zasu iya hanawa a rantsar dani a wannan wata ~Cewar Bola Tinubu
Bola Tinubu daye magana ta Bakin Kakakin Kamfen din Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, ya yi fatali da matakin da wasu ke Shirin dauka na dakatar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kafin ranar 29 ga watan Mayu.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, jigon na APC ya bayyana cewa an kai wasu jami’an shari’a zuwa kasar domin cimma wannan manufa.
Keyamo ya siffanta tunanin a matsayin jahilci, yana mai cewa “masu hali na rashin mutunci suna cin gajiyar wadannan talakawa”.
Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Na karanta wani wuri cewa wasu da ake zaton sun koya ne ke tabbatar wa masu yada labaran cewa za a iya dakatar da bikin rantsar da @officialABAT a bisa doka kafin ranar 29 ga Mayu da kuma wani labari cewa an kai wasu lauyoyin kasashen waje domin cimma wannan manufa. Kuma na karanta da yawa m halayen daga twits.
Sai na girgiza kai na yi ta gunaguni a raina, ‘Gaskiya jahilci cuta ce kuma abin bakin ciki ne yadda wasu marasa mutunci ke cin gajiyar wadannan ’yan uwa talakawa.
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta sanya ranar Litinin don fara sauraron karar da ‘yan takarar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyyar Labour ta Peter Obi suka shigar domin kalubalantar nasarar Tinubu.
A halin da ake ciki dai, Aso rock ya saka sabon salo a yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen mika mulki cikin lumana a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin mika mulki ga Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.