Labarai

Na koma APC domin na Zama Gwamnan Adamawa.

Spread the love

Sanatan da ke wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo, ya bayyana cewa ya fice daga Jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyyar All Progressives Congress, domin cimma burin sa na zama Gwamna a 2023.

Abbo, wanda shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya karanta wasikar ficewarsa a zauren majalisar dattijai a ranar Laraba, duk da haka ya dage a taron manema labarai bayan taron, cewa akwai babbar matsala a wani bangare a jihar ta Adamawa.

Ya kuma ce bai shirya yin murabus ba a matsayin Sanata kamar yadda PDP ta nema.

Sakataren Yada Labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, yayin da yake mayar da martani game da sauya shekar Abbos ya ce, “Sanata Abbo, yana sane da yadda tsarin mulki ya nuna shawarar da ya yi na sauya sheka zuwa wata jam’iyyar; wanda shi ne, ba zai iya ci gaba da mamaye kujerar PDP a Majalisar Dattawa ba.

“Wurin duk wani Sanatan da ya canza jam’iyya sai dai kawai a bisa dalilin da Kundin Tsarin Mulki ya bayar a bayyane yake kuma PDP ba za ta bar Sanata Abbo ya gudu da aikin da aka bashi ba.”

A martanin da ya mayar, Abbo ya ce, “Shin sun nemi (Gwamna Dave) Umahi ya yi murabus? Je ka tambaye su (PDP). Gwamna Umahi kawai ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a matsayin gwamna mai ci a jihar Ebonyi. Shin sun nemi ya yi murabus?

“Akwai rikici a cikin jam’iyyar (PDP) a jiha ta. Gaskiya kenan. Na yi imanin dimokiradiyyar cikin gida a cikin jam’iyyar ta wahala a cikin shekara guda da ta gabata lokacin da gwamnan ya hau mulki.

“Kamar yadda duk kuka sani, a jihar Adamawa ne kawai muka sake fasalin PDP. Akwai rikici a cikin jam’iyyar a jihar Adamawa kuma gwamna ne musabbabin rikicin. ”
Tun da farko, a cikin wasikar ficewarsa wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya karanta a zauren majalisar dattijai, Sanatan ya ce, “A yau, na shiga APC da Shugaban Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari, gina kasar mu na Najeriya. ”

A yanzu APC na da sanatoci 60, yayin da PDP ke da 42. A yanzu haka akwai kujerun majalisar dattijai shida.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button