Labarai

Na Rantse Da Allah Da Ni Ne Shugaban Kasarnan Da Tuni Boko Haram Ta Zama Tarihi, Inji Atiku Abubakar.

Spread the love

Na Rantse Da Allah Da Ni Ne Shugaban Kasarnan Da Tuni Boko Haram Ta Zama Tarihi, Inji Atiku Abubakar.

Da yake mika sakon jaje ga gwamnan jihar Borno tare da yiwa iyalan wadanda aka kashe a harin kwanton bauna da ‘yan Boko Haram suka kai kan tawagar gwamnan ta’aziyya,, tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce da ace shine shugaban kasa da tuni ya gama da Ƙungiyar Boko Haram.

Atiku Abubakar ya kuma yi rantsuwa da girman Allah cewa inda shine shugaban kasa da tuni boko haram ta zama Tarihi a Najeriya.

Ya ce domin shi maganin Biri Karen Maguzawa ne, inji Atiku Abubakar.

Alhaji Atiku Abubakar dai shine tsohon Mataimakin shugaban Kasa a zamanin gwamnatin Obasonjo, haka zalika ya yi takarar shugabancin Kasa a shekarar 2011 a ƙarƙashin jam’iyyar ACN, Sannan kuma ya tsaya takarar shugabancin Kasa a Zaben da ya gabata na Shekarar 2019, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, kuma har Yanzu yana da muradin zama shugaban Kasar Najeriya.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button