Labarai

Na tabbata Dan takarar Jam’iyarmu na Apc Ahmad Ododo ne zai lashe zaben Gwamnan jihar Kogi a zabe Mai zuwa ~Cewar Bola Tinubu.

Spread the love

A wata sanarwa da Sakataren Yada labarai na gwamnan jihar Kogi ONOGWU Mohammed ya fitar Yana Mai cewa Zababben shugaban kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya Saka albarka tare da nuna goyon bayansa ga Hon. Ododo Ahmed Usman, OAU, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kogi 2023, yayin da yake tabbatar masa da samun nasara a zaben watan Nuwamba.

A ziyarar da Ododo ya kai gidansa da ke Abuja ranar Asabar, Asiwaju ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar a jihar da su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben. Ya bayyana cewa Kogi ta kasance tungar APC da ke da riko da nasarorin zabe tun 2015 kuma ya bayyana ko shakka babu Ododo zai yi nasara a watan Nuwamba. Zababben shugaban kasar ya kuma yabawa shugabannin jam’iyyar da magoya bayansa bisa gagarumin nasarar da suka samu a zaben da ya gabata.

Tun da farko, Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, wanda ya jagoranci Ododo a ziyarar, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar sun zabi Ododo ne a matsayin dan takarar bisa la’akari da iyawarsa da kwarewarsa da kuma iya shugabanci yadda ya kamata. Ya kuma tabbatar wa Asiwaju cewa al’ummar jihar Kogi za su kada kuri’a don ganin an samu hadin kai, wanda takarar Ododo ke wakilta, ganin irin ci gaban da aka samu a jihar cikin shekaru bakwai da suka gabata.

A ranar 14 ga Afrilu, 2023, kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC reshen jihar Kogi ya ayyana Alhaji Ahmed Usman Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan APC na jihar Kogi, bayan da ya samu kuri’u 78,704 inda ya doke sauran ‘yan takara a zaben.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button