Labarai

Na tabbata Gwamna El’rufa’i Zai kawo karshen Ta’addancin jihar kaduna-Sanata uba Sani

Spread the love

Sanata Uba Sani, Mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a zauren Majalisar dattijan Nageriya Kuma shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan banki, Inshora da sauran harkokin kudi. Ya yi magana da manema labarai a Majalisar Wakilai ta kasa kan kokarin da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa yake yi don magance matsalar rashin tsaro a Kudancin Kaduna dama baki dayan jihar ta Kaduna Dan Yan jaridar Suke tambayar sanata Uba cewa tsawon Shekara daya na zamanka a cikin majalisar dattijai kuma gashi dai an riga an nada ka a matsayin daya daga cikin sanatocin da suka fi aiki a kasar. Menene sirrin?

Sanatan yace Ba zan yi maku karya ba; ba Abu bane da zai kasance da sauƙi tun daga ranar Dana zama sanata daidai da Rana Daya ban taba hutawa ba saninku ne Mun rasa wakilcin mai inganci a Majalisar ta 8. Bana daga cikin masu zaman kashe wando a Majalisa kamar irin wa’yanda suka gabata,, ka tuna fa anyi Sanata a majalissar ta 8 daya fito fili ya yaki aminta kan batun karbo babban bashi wanda aka riga aka shirya shi domin inganta kiwon lafiya, ilimi da sauran muhimman ababen more rayuwa a jihar Kaduna Amma duk da haka Wasu mutanen kiran wannan matakin suke a kan gwagwarmaya, Maganar Gaskiya aiki da rashin gaskiya da kuma wuce gona da iri na wasu mutane ba gwagwarmaya bace. Kishin gwagwarmaya nada daraja amma Wadanda suka san ni da kyau, suna iya tabbatar da gaskiyar cewa baki dayan galibin rayuwata, na kasance cikin gwagwarmaya. Ko a yau, zaku iya ambatana da Suna dan gwagwarmaya a fagen siyasa. Na ji akwai bukatar gaggawa a tsara wata hanya ta daban don ci gaban mutanen mu a Jihar Kaduna baki daya. Don haka, don amsa tambayar ku, Ina da dalilai biyu masu mahimmanci: na farko shi ne cewa mu (Kaduna ta Tsakiya) mun rasa abubuwa da yawa a cikin Majalisa ta 8 data gabata saboda haka ya zama wajibi mu hanzarta kokari a Majalisar ta 9. Abu na biyu, Ina samun kwarin gwiwa daga wajen shugabana, abokin rikon amana, Mallam Nasir El-Rufa Gwamnan jihar Kaduna. Idan mutumin da ya hore ka bai huta ba, ban tsammanin zai yi ma’ana ba kaima ka huta, A koyaushe na san cewa muna da abubuwa da yawa da za mu iya ingantasu ga mutanen kirkinmu na jihar Kaduna Tabbas muna kokari tare da gaggautawa Don saka Kaduna sahun farko Kan sauran jihohin Najeriya.

Dan jarida yace kana daga cikin sanatoci uku Wanda aka saka sunansu da suka fi kawo kudrin lissafin kirkirar sabon Al’amari Bill) a Majamajalissar dattijan ko? Sanatan uba Sani yace Haka ne, Gaskiya ne Ina cikin su kuma ina mai farin ciki da cewa kudrin Bill) guda biyu yanzu haka sun tsallake dukkan sharuda a Majalisar kuma an zartar dasu cikin doka. Kamar yadda zaku iya sani, Bill din guda biyun sune Bill din Kafa Kwalejin Ilimin ta Tarayya a Karamar hukamar Giwa, wanda Yanzu haka an zartar dashi acikin doka a ranar Laraba 15 ga Yuli, 2020 Sai kudri na biyu wanda na hada hannu tare da Sanata Betty Apiafi, ita ce Dokar da ke kunshe da za ta sake bunkasa Bankuna da sauran Ma’aikatun Kasuwanci na 2004 da kuma sake yin amfani da Dokokin Banki da Sauran Dokokin Masana’antu da Sauran batutuwa Wanda suka zo zuwa shekara ta 2020, wanda majalisar ta zartar a ranar Alhamis, 23 Yuli 2020. Kamar yadda na faɗi cewa ilimi matsayina Kan Batun habbakawa da bunkasa harkar ilimi a Arewacin Najeriya baki daya da kuma jihar Kaduna musamman, kokarinda nakeyi kai tsaye da kuma karfafa tunani game da tabbatar tare da kuma babban aiki wanda Gwamna Nasir El’rufa’i yakeyi na Shirin farfado da Ilimin a jihar Kaduna. Wanda tunanin nasa na farfado da ilimi tuni ya samu karbuwa. Yanzu haka Jihar Kaduna ta zama abin koyi ga gyaran harkar ilimi.
Ba zan taba yin watsi da bin Jagoran gwamna ba. Na sha alwashin yin duk abin da ake bukata don tabbatar da kyakkyawar makoma ga yaranmu ta hanyar ilimi. Ina kuma da yakinin cewa da zarar an kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Giwa, za ta bunkasa matsayin Giwa da sauran al’ummomin dake makwabta da garin na giwa Hakanan Kuma yanzu yana da matukar mahimmanci a gare ni nayi ƙoƙarin tare da hazikan ma’aikatana domin ganin an aiwatar da ƙarshen waɗannan kudirin cikin doka. Musamman, ina mai matukar godiya da irin kokarin da mataimakana irinsu Bello El Rufa’I, Abdul Azeez Ojelade, Yvonne Okeke, Olaitan Fajuitan, Eng. Jamilu Ahmed kuma ba shakka mutane ne masu rikon Amana da rikon aikin su da Gaskiya da sauran su dai dukda Ofishina yana kama da karamar Najeriya. Ina jinjina ga dukkan su; sun ba da gudummawa sosai ga nasarar da na samu a majalisar dattijan Nageriya.

KAN BATUN TSARO SANATA UBA SANI YACE

Mun ci gaba da mai da hankali kan abin da muke tunani da burinmu duk da yanayin rashin tsaro da ke faruwa a Kudancin Kaduna. Gwamnatin Jiha tare damu matuka muna daukar dukkan matakan da suka wajaba don kawo karshen lamarin. Amma, nasan zaku yarda da ni cewa rashin fahimta da kuma bayyana bayanai game da manufofin gwamnati yasa aka samu koma baya.ku sani hatta yara a makarantun firamare da sakandare suna sane cewa al’umma na fuskantar matsalar tsaro ta kasa. Wanda tushensa ya fara daga Arewa maso gabas tare da hare-haren Boko Haram musamman jihohin Borno da Yobe Abin da na yi imani dashi shine cewa masu taurin kai da ‘yan fashi sun Karya lagon kokarinmu kan ayyukan tsaro a Arewa maso Gabas, musamman jihohin nan biyu, Gwamnan jihar Katsina yana kuka kusan kullun; kan ire iren tashin hankali dake faruwa ajiharsa ga jihohin Benue, Nassarawa da Filato. Sannan kuma kuna sane cewa Gwamnan jihar Zamfara shima yana korafi Gwamnan jihar Kano wani lokaci shima yana korafi akan wadannan masu aikata MUGGAN laifuka da ‘yan fashi. Amma nasan Kuma sane da tarihin Jihar Kaduna, lokacin da masu laifi da ‘yan fashi suka fara a Kaduna, sai ake yawan tunanin cewa rikicin addini ko kabilanci ne Sanata, shin kana cewa rikicin yankin Kudancin Kaduna ba shi da nasaba da kabilanci ko addini?
Sanata Uba sani yace ni Dan Jihar Kaduna ne kuma ina magana da gwamna na kullun; Ina magana da shugabannin al’umma da shugabannin addinai yau da kullun, musamman ganin yadda
Yanki na gundumar na fama da rashin tausayi na wannan rikice-rikicen da ba dole ba. Yanzu, masu laifin za su yi bore ne ga al’ummomi a cikin garin Kaduna, yadda suke yi a garuruwa jihohin Katsina, Nassarawa, Zamfara da sauran jihohin da ke Arewacin Najeriya kuma abu na gaba da za ku shaida a Kaduna shi ne cewa mutanen da ke cin gajiyar rikicin kabilancin da addini alamu ya nuna cewa yanzu zasu fara kiran Jama’a ne Kan addinai da ban daban, Abin da ya dace ga Jama’a yanzu a cikin wannan yanayi shi ne kowa da kowa ya hada hannu da gwamnan Jiha da jami’an tsaro na kasa don korar wadannan ‘yan fashi daga cikin
Yankinmu.

Jihar Kaduna ta sha wahala sosai saidai. Labari mai dadi shine cewa gwamna El-Rufai ya yanke shawarar game da shirya tsaro da takaitaccen bayani a jihar Kaduna. Yanzu mun gudanar da taron nesa nesa wanda ke da dukkanin manyan ofisoshi da masu rike da mukaman siyasa, ba tare da la’akari da jam’iyya ko addini ba Wanda ya gudana a ranar Asabar, 15 ga Agusta 2020. Kowanne mutum daga Mataimakin Daraktan gwamnati a Gwamnatin Tarayya ko na Ma’aikatan Rundunar Jiha; duk masu rike da mukaman siyasa wadanda aka zaba ko aka nada, Gwamnan ya saukar da kansa cewa a shirye yake ya yi na’am da sukar, kowa a kowane yanki kowa ya ji cewa Duk mutanen da suka halarci taron nesa nesan sun gigice sosai bayan sun gano gaskiya A zahiri, na tausaya wa Mallam Nasir El Rufai. Domi Ban ga wani shugaba a Najeriya da ba a fahimta ba kamar Malam Nasiru abinda mutane Basu sani ba shine. Mataimakan Mallam Nasir El Rufai galibi Kiristoci ne daga Kudancin Kaduna. A zahiri, sama da kashi 15 na membobin majalisar gwamna El-Rufai basu a tsakiyar kaduna. Ba’a fahimce shi sosai ba kuma ina ganin wannan ba adalci bane.

Shin ba an yayata cewa Malam El-Rufai yana son kujerar shugaban kasa ba? Amma lokacin da ya fito fili yayi Maganar ya ce lokaci ya yi da ‘yan Kudu zasu Shugaban ci Nageriya bayan Shugaba Buhari, sai kuma wasu mutane suke sake cewa: wai wannan wanne irin mutum ne haka? Yana rikitar da mu. ” Maganar gaskiya ita ce gwamna Nasir El-Rufai ba mutum bane mai wasa mutum ne mai cikakken hankali. Ba wai saboda shi babban abokina ba, na yi alwashin cewa a karkashin Mallam Nasir El-Rufa nake, jihar Kaduna a halin yanzu ita ce mafi kyawun jihar da ake shugabanta a Najeriya. Ba da jimawa ba ne, Hukumar Kula da Inshora ta Kasa (NDIC) ta shirya wani tunanin tuna baya cikin mambobin kwamitin Majalisar Dattawa kan banki, Inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade, wanda na ke shugabanta, Sanatoci sun firgita da irin ci gaban da suka ga an samua jihar ta Kaduna. Ayyukan manyan hanyoyi, cibiyoyin ilimi da kiwon lafiya na jihar. game da sauye-sauye mahimmin fannoni irin su biyan haraji da kuma saukaka harkokin kasuwanci Kaduna ta dade da kammala Shirin Samun rahusa na yin ka’idodin kasuwanci kafin Gwamnatin Tarayya ta fara tunanin hakan. Su kansu Sanatocin da sukaji sai da suka firgita da gano cewa jihar Kaduna ta zama babbar cibiyar hada-hada, ba iya Najeriya ba kawai harzuwa yankin na Afirka ta Yamma baki daya. Bugu da kari, da yawa daga cikin Sanatocin sun firgita lokacin da suka ji hakikanin gaskiyar labarin rikicin Kudancin Kaduna daga Gwamna da wasu majiyoyi da yawa yayin ziyarar. Sunsha mamaki da sukaji yadda wasu yan siyasa masu hargitsi da Suke amfani da rikicin wajen cimma manufarsu ta siyasa. shin jami’an tsaro, musamman Sojojin Sama, suna yin abin da ya isa ya taimaka wajen dakile mummunan halin da ake ciki a Kudancin Kaduna? Kun sani, kasancewata sanata yana sanya ku a wani zama cikin yanayi maikyau Ina da bayanai sosai a wurina. Lokacin da ni ba dan majalisar dattijai ba ne, amsata ga tambayar ku ta kasance daban. Amma yanzu nasan shine lokaci mafi kyau na baku amsa Mai kyau, A zahirin gaskiya, jami’an tsaron mu sun mamaye. Ko’ina Suna yin yaƙe-yaƙe na cikin gida da yawa a cikin jihar.

Dole ne mu ci gaba da karfafa su; Ya kamata mu a cikin Majalisar Dattijan ta kasa su nemi hanyoyin wasu kudade don horarwa da kayan aikin Sojojinmu. Suna kuma buƙatar horo da yawa a cikin yaƙin nasu. Misali, a jihohin Borno, Yobe, Nassarawa har ma a cikin Kaduna, masu tayar da kayar baya da ‘yan fashi da suke fafatawa da su suna aiki a cikin wasu wurare masu hadari. Dole ne mu dawo da tsaronmu da sojojin mu a cikin yaƙin da .suke. Koyaya, ne jihar Kaduna, ku godewa Allah saboda tattaunawar da aka dade ana yi tsakanin Shugabanmu Gwamnanmu da shugabannin rundunonin sojojinmu, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da tura runduna ta Musamman daga Rundunar Sojan Sama ta Najeriya don hada kan kokarin dakile ayyukan. ‘yan fashi a Kudancin Kaduna. Sojojin musamman na Sojan Sama sun zo Kaduna bayan takwarorinsu na Sojojin Najeriya sun isa Kafanchan tun da farko. Don amsa tambayarku, jami’an tsaronmu suna iya bakin kokarin su duk da matsalolin da na lissafa a baya. Koyaya, matsalar Kudancin Kaduna ba za’a warware ta gaba daya ta hanyar yakin zahiri ba. Har ila yau rikicin yana da abubuwan da suke Kara Hura wutarsa Wato Siyasa tare da addini. Hakan haɗari ne mai munin gaske, idan kun san abin da nake nufi. Wannan shine ainihin abin da gwamna El Rufa’i ya kuduri aniyaryi. Kuma ya gudanar har’ila yau yanzu yana kan gudanar da tarurruka kala kala tare da shuwagabannin Kiristoci da na Musulunci masu daraja. Gwamnan kuma ya tattauna da shugabanin jihohi da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya, da kuma manyan malaman islama,

Matsalar Kudancin Kaduna abu ne da za a iya shawo kan shi da zarar mun sami damar dakatar da wasu ‘yan siyasa marasa galihu da kuma rikice-rikicen masu fafutuka da muzgunawa mutanenmu. Jihar ta kaduna abar alfaharinmu yanzu Haka Ba mu da wata jiha da zamu amsa kiranta kamar kaduna, Rashin tsaro abu ne mai hana ci gaba Dole ne mu hada karfi da karfe don samar da zaman lafiya a Jihar kaduna dama arewa izuwa ko’ina a sassan Nageriya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button