Na Yarda Zan biyaka N160,000 idan kaima za ka iya biyan ku’din gamsar da Kai da nayi a lokacin Jima’i mata mai neman saki ta fadawa mijinta a Kotu bayan yace ba zai saketa ba sai ta biya shi ku’di.
Hauwa Hamza ta garzaya wata kotun koli da ke Kubwa a babban birnin tarayya Abuja, inda take neman a raba aurenta da mijinta Yahaya Mohammed, bisa dalilan rashin kulawa da mutuntawa.
Mista Mohammed da Ms Hamza, sun yi aure ne bisa tsarin shari’ar Musulunci a wani lokaci a shekarar 2020 kuma ba su da ‘ya’ya tare.
Amma mijin wanda dan kasuwa ne, ya shaida wa kotun cewa zai amince da bukatar saki idan matarsa za ta biya shi kudi N160,000 da ya kashe mata.
Idan tana son saki sai ta auro min wata mata. Ina son matata ta biya ni duk abin da na kashe mata a bikin aurenmu.
“Na biya N60,000 a matsayin sadaki don in auri matata kuma na kashe Naira 100,000 na kayan sawa, nace ta biya mani jimillar kudaden,” in ji shi.
A martanin da ta mayar, mai shigar da karar ta ce idan har Musulunci ya dace ta auri mijinta kafin ya sake ta, sai ta yi hakan.
Ta kara da cewa Mista Mohammed bai kashe mata kudi har N160,000 ba, inda ta ce sadakinta ya kai N60,000 kacal.
“Ba ni da Naira 160,000 da zan ba shi, sai dai idan shi ma zai iya biya ni don biyan bukatar da na yi masa a lokacin aure da kuma girkin da na yi tsawon shekaru,” in ji mai karar.
Mista Mohammed, ya ce idan mai karar ya ce ta gamsar da shi, shi ma ya kula da ciyar da ita da jin dadin zaman auren.
Alkalin kotun, Mohammed Wakili, ya ce bai dace a addinin Musulunci ba a ce mai karar sai ta samo wata matar kafin ya raba auren.
Mista Wakili ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga Oktoba domin yanke hukunci.
NAN