Labarai

Na yi imani Jam’iyar APC ce zata lashe Zaben kananan hukumomi 44 da akeyi a jihar Kano ~Inji Abdulmumin Jibrin.

Spread the love

Tsohon Dan Majalisar kananan hukumomin Bebeji Kiru a jihar Kano ya ce yayi Imani da Cewa Jam’iyar APC ce zata kashe Zaben kananan hukumomi a Kano tsohon Dan Majalisar Kuma Daraktan gidaje a yanzu ya rubuta a shafinsa na Twitter Yana Mai Cewa A yau kamar yadda na saba, daga gida na a garin Kofa Bebeji, na biya gidan mu na gado kafin naje rumfan zabe na kada kuria ta ga jamiyyar mu ta APC a zaben da ake gudanarwa na Shugabannin Kananan Hukumomi da Kansiloli.

Ina da kwarin gwiwa cewa jamiyyar APC zata samu nasara ba wai a kananan hukumomin Kiru da Babeji ba kadai harda jihar Kano gaba daya.

Na kuma tabbatar da anyi zabe cikin kwanciyar hankali muna mika godiya ga maigirma gwamna da jam’iyya, jami’an tsaro, da hukumar zabe na ganin anyi zaben cikin kwanciyar hankali.

A yau kamar yadda na saba, daga gida na a garin Kofa Bebeji, na biya gidan mu na gado kafin naje rumfan zabe na kada kuria ta ga jamiyyar mu ta APC a zaben da ake gudanarwa na Shugabannin Kananan Hukumomi da Kansiloli. Ina da kwarin gwiwa cewa jamiyyar APC zata samu nasara ba wai a kananan hukumomin Kiru da Babeji ba kadai harda jihar Kano gaba daya.

A sakamakon girma da yake kamani da kuma hikimomi da nake samu, na dauki falsafar siyasar gogaggen dan siyasar nan Marigayi Waziri Ibrahim ta yin Siyasa Bada Gaba Ba. Wannan shi zai cigaba da daurani akan yanda zan cigaba da gudanar da siyasa ta har Illa Masha Allahu da izinin Allah Subhanahu Wa Taala.

Ni mutum ne me fatan ganin gobe tayi kyau a koda yaushe, idan akayi amfani da abubuwan da suka dace, matsaloli da kalubalen da kasar nan take fuskanta za a shawo kansu. Insha Allahu zamu rayu muga Nigeria me kyau wacca muke fata. Amin Ya Rabbi

Hon Abdulmumin Jibrin
Kofa, Bebeji, Kano
16-1-2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button