Nagari Na Kowa. Alh. Auwalu Abdullahi Rano (A.A Rano).
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi
Attajirin Dan Kasuwa Ne Shi Abin Kwatance, Wanda Yake Kokari Matuka Wajen Taimakon Al’umma.
A Binciken Da Na Gudanar, A Kullum Daga Gida Zuwa Office Yana Magance Matsalolin Mutane Bila Adadin, Wanda Ko Shi Bai San Adadinsu Ba.
Duk Da Tulin Ayyukan Da Sukayi Masa Yawa, Hakan Bai Hanashi Kirkiro Hanyoyin Tallafawa Mabukata Ba, Da Tabbatar Da Cewa Wadanda Suke Amfana Da Tallafin Da Yake Bayarwa Sun Can-canci A Tallafa Musu.
Alh. Auwalu Abdullahi Rano (A.A Rano), Mutum Ne Wanda Yake Taimakon Al’umma A Fili Da Sarari, Dare Da Rana, Kusan Ko Da Yaushe Idan Kaganshi Za Ka Iskeshi Tare Da Jama’a Masu Neman Taimako, Kuma Sai Ya Yayewa Kowa Matsalarsa.
Ayyukan Alkhairan Da A.A Rano Yake Yi Ba Za Su Lissafu A Wannan Takaitaccen Rubutun Nawa Ba, Sai Dai Mu Dauki Kadan Daga Ciki…..
Alh. Auwalu Abdullahi Rano Ya Kasance Yana Rabawa Mabukata Kayan Abinci Da Kudi Lokaci Zuwa Lokaci, Wanda Ko A Satin Da Ya Gabata Ma Labari Ya Iskeni Cewa Ya Rabawa Al’ummar Garin Rano Buhhunan Shinkafa Da Naira Dubu Ashirin Ashirin, Malam Ka Ji Yadda Ake Yin Kyauta, Abaka Abinci Sannan Kuma Abaka Kudin Cefane…
Banda Garinsa Na Rano, A Duk Shekara Yakan Raba Kayan Abinci Da Kudi A Kananan Hukumomin Jihar Kano A Kalla Guda Uku Ko Hudu, Wasu Sukan Sami Buhun Shinkafa Da Dubu Hamsim, Wasu Da Naira Dubu Ashirin Wasu Kuma Da Dubu Goma…
Wani Bawan Allah Da Yataba Rabauta Da Kyautar Naira Dubu Hamsim Daga Attajiri Alh. Auwalu Abdullahi Rano Ya Shaidamin Cewa Shi Bai San A.A Rano Ba, Haslima Bai San Wasu Daga Cikin Makusantansa Ba Balle Ace Kyautar Sanayya Akayi Masa.
Suma Kananun Ma’aikatan Da Suke Aiki A Kamfanin A.A Rano Sun Bayyanamin Yadda Suke Samun Walwala Da Jin Dadin Aiki A Kamfanin, Saboda Yadda Yake Inganta Rayuwarsu. Wannan Kadan Kenan…
Wani Gagarumin Aikin Taimako Da Jinkai Da Attajiri Alh Auwalu Abdullahi Rano Yayi Shine Kafa Gidauniyar Tallafawa Mabukata Ta A.A Rano Foundation Da Yayi, Wadda Take Aiki Ba Dare Ba Rana Wajen Bada Tallafi A Fannin Lafiya Da Ilimi:-
Gidauniyar Tallafawa Mabukata Ta A.A Rano Foundation An Kafata Ne Domin Taimakon Marasa Lafiya Wadanda Basu Da Halin Zuwa Asibiti, Ko Kuma Basu Da Halin Biyan Kudin Da Aka Nema A Asibitin.
Gidauniyar Wadda Take Gudana Karkashin Jagorancin Jajirtaccen Alh. Abdallah M Abdallah Tana Da Kyakkyawan Tsari Wanda Ya Saukakawa Al’umma Samun Tallafi Daga Gareta. Haka Kuma Ba Iya ‘Yan Kano Wannan Gidauniya Take Taimakawa Ba, Har Da Sauran Garuruwan Najeriya. Kai Ko Iya Wannnan Gidauniya Kadai A.A Rano Yakafa Ya Can-canci Yabo. Allah Yasaka Masa Da Alkhairi Amin.
Daga Edita Sabiu Danmudi Alkanawi…

