Labarai

Nageriya ta bawa Africa da duniya kunya ~Cewar Obasanjo.

Spread the love

Obasanjo ya yi magana a wajen taron baje kolin wani littafi mai suna ‘Reclaiming Jewel of Africa’ wanda tsohon ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Olusegun Aganga ya rubuta. An gudanar da taron ne a Abuja.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa kasar Nageriya ta bawa Afirka da ma duniya kunya.

Ya kuma dora alhakin ci gaban al’ummar kasar a kan rashin daidaiton manufofin gwamnatocin baya.

Bayan Obasanjo, tsohon shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan, wanda shi ma ya yi magana ya bayyana cewa daidaiton manufofi da aiwatar da shi da kuma daidaiton Al’umma dole ne ya zama abin lura ga kowace gwamnati.

Shugaba Bola Tinubu, wanda mashawarcinsa na musamman kan harkokin kudi Olawale Edun ya wakilta a wurin taron, ya bayyana irin matakan da ya kamata Nijeriya ta bi domin samun dogaro da kai.

Tsofaffin ministoci da shugabannin jami’an gwamnati, jami’an diflomasiyya, da sarakunan gargajiya na daga cikin bakin da suka halarci bikin kaddamar da littafin.

Aganga, marubucin, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta fito da tsare-tsaren da za su sa jarin ya bunkasa.

Littafin ya yi nazari ne kan yadda Najeriya za ta iya zama a matsayinta na Daya daga kasahen duniya ta hanyar bin ka’idojin da za su yi tasiri ga ci gabanta.

Har ila yau, yana ba da tambayoyi da mafita ga harkokin mulki da yadda za a inganta al’umma wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button