Labarai

Nageriya tayi Asarar naira Tiriliyan N16.25tr domin satar danyen mai.

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta Bakin Babban Sakatare Kuma Shugaba na Najeriya Extractive Industries Transparency Initiative (NEITI), Ogbonnaya Orji, ya ce Najeriya ta yi asarar sama da Naira Tiriliyan 16.25 sakamakon satar mai a kasar.

Orji a rahoton da ya aikewa shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar, Bamidele Salam, a yayin wani zaman tattaunawa da aka yi a Abuja, ya kuma ce an kashe dala biliyan 74.386 kan tallafin man fetur da gwamnatocin da suka shude suka yi tun daga shekarar 2011.

A cewarsa, hukumar ta tattara ainihin adadin kudaden da ake biya a matsayin tallafi a duk shekara. Orji ya yi ikirarin cewa an tattara bayanan ne bisa bayanan da masu gudanar da masana’antar da sauran masu ruwa da tsaki suka sanyawa hannu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button